Na Yi Nadamar Shigar Nuna Tsiraici Da Na Yi – Rahama Sadau

Jarumar Hausa Film ta Kannywood, Rahma Sadau, ta fito fili ta yi magana a kan sukar lamirin da aka yi ta yi wa hotunan da ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani wadda ke nuna tsiraicin ta a fili.

Idan ba’a manta ba, hotunan jarumar sun yi ta yawo a kafafen sada zumunta, bayan ta wallafa su, har mutane suka yi ta cewa sun saba wa addini da al’adarta.

Jarumar ta kara wata wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda tace tayi dana sanin wallafa hotunan da suka janyo tsokaci na sabon Allah da manzonsa, inda tsame kanta daga wadannan munanan kalamai.

“Salam, a gaskiya ban ji dadin ganin sakonni da cece-kuce a kan hotunan da na wallafa da a ganina basu da wata illa ba.
A matsayina na ‘yar adam, na yi dariya a kan wasu tsokacin wasu kuma sun sani takaici da alhini. Wadanda suka fi tayar min da hankali sune yadda wasu suka sauya salon al’amarin gabadaya.
“Ina da mabiya masu addinai daban-daban wadanda wasu suka yi tsokaci na sabon Allah, sai dai in ce subhanallah.

Wasu kuma suna ?o?arin kalaman ?atanci Ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) – Wannan shine kololuwar sabon Allah, wanda ya ja nayi dana sanin wallafar tawa gabadaya.

“Duk wanda ya san ni ya san cewa bana tanka wa kowa koda zagina yayi, Amma a kan Annabina da addinina dole ne in dakatar da ko wanene. “Ba zan lamunci zagi ko kuma cin zarafin addinina ba, ko wanene kuma a ko ina ne.

“Duk wadanda suka yi wannan su kiyaye, kuma yakamata su san darajar addinai. Ni mai kare martabar addini na da manzo na ce a duk inda na tsinci kaina.”

Related posts

Leave a Comment