Tsohon jami’in dan Sanda Mista Fulani Kwajafa yace an kirkiri rundunar SARS ne domin yaki da fashi da makami a fadin kasar nan, da nufin dawo da ƙasar kan saiti.
Fulani Kwajafa, tsohon dan sanda ne wanda ya jagoranci kirkirar SARS, ya nuna nadamarshi na kirkirar rundunar a hirarsa da BBC Hausa a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba. Ana tsaka da zanga-zangar rushe rundunar.
Kwajafa yace an kirkire su ne don yaki da fashi da makamai a fadin Najeriya. Kwajafa ya sanar da yadda aka kirkiri SARS a shekarar 1984, lokacin Etim Inyang ne sifeto janar na ‘yan sanda lokacin Buhari na Shugaban kasa na mulkin soji.
“Amma sai dai daga labaran kungiyar da nake ji, sun canja salon aikin nasu, duk sai naji takaici da danasanin kirkirar kungiyar,”
Tun daga ranar Alhamis din makon da ya gabata ne matasa a yankin kudancin kasar nan da babban birnin tarayya suke zanga-zanga. Suna yin hakan ne domin neman a rushe runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makamai a fadin kasar nan.