Na Tuba Da Yin Siyasa – Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya ce ba zai sake tsaya wa takarar zabe domin neman kujerar shugaban kasa ba, domin yin haka zai dakushe kimarsa a idon jama’a.

Jonathan wanda ke tsokaci akan wani littafin da aka wallafa akansa wanda ya mayar da hankali akan zamansa a fadar shugaban kasa, yace zubar da kimarsa ne ya koma yana rokon mutane domin marasa baya da kuma masa yakin neman zabe domin sake zama shugaban kasa.

Tsohon shugaban yace muddin jama’a suka farka a baci suka ganshi ya sake zama shugaban kasa, toh babu tantama wani yanayi ne da yafi karfinsa, kuma babu yadda zai iya yi, a maimakon yin gaban kansa wajen sayen fom na tsayawa zabe da zuwa wuraren jama’a domin neman su mara masa baya.

Jonathan yace ba zai sake takarar zabe ba a Najeriya ba, yayin da ya bayyana yadda yake kallon mutane suna ta wasan kwaikwayo dangane da rade radin cewar zai sayi fom domin takarar zaben shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC a watannin da suka gabata.

Idan ba’a manta ba, a watan Yunin da ya gabata, wata kungiyar makiyaya da almajirai a karkashin Ibrahim Abdullahi ta lale naira miliyan 100 wajen saya masa fom domin tsayawa takara a Jam’iyyar APC.

Tsohon shugaban yace yayi ta mamaki lokacin da ake dambarwar dangane da rade radin takarar tasa, musamman ganin yadda aka kore shi a ofis cewar bashi da kwarewar da ake bukata na shugabanci, amma kuma sai ga wasu sun dawo suna wanke masa sunansa.

Jonathan yace yanzu aikin da yafi dacewa da shi shine tabbatar da dimokiradiya a kasashen Afirka dake fama da matsaloli, kuma a shirye yake ya tafi kowacce kasa dake fuskantar irin wannan kalubale domin samar da yanayi mai kyau da za’a samu zaman lafiya.

A karshe, tsohon shugaban ya bayyana damuwarsa dangane da tsayar da ‘yan takarar shugaban kasa da mataimaki daga addini guda a Jam’iyyar APC, sabanin yadda aka saba yi a Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply