Na Tuba Da Yin Fim: Maryam Yola

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Maryam AB Yola, ta fitar da sanarwa a shafinta na Instagram inda ta ce daga ranar 1 ga watan Satumban 2020, ta fice daga masana’antar Kannywood.

Daga karshe ta mika godiyarta ga masoyanta, kawaye da abokan arziki a kan irin kaunar da ake gwada mata.

Kamar yadda ta wallafa a shafin nata, “Assalamu alaikum. Ni Maryam AB Yola ina mai sanar da ku cewa daga yau daya ga watan Satumban 2020, na daina yin fim kuma na bar Kannywood.

Kuma ina matukar godiya da kaunar da kuke nuna min. Allah yasa mu dace, Ameen.

Jarumar wacce tsohuwar mata ce ga fitaccen jarumi Adam A. Zango, mazauniyar garin Abuja, ba ta sanar da dalilin ta na yanke wannan hukuncin ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply