Na Tayar Da Matattu Sama Da 50 Bayan Sun Mutu Murus A Coci Na – Fasto Chris

IMG 20240324 WA0040

Babban malamin Cocin Christ Embassy, Chris Oyakhilome, ya tada kura bayan kalaman da ya yi a baya-bayan nan, lamarin da ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta. A yayin wata addu’ar waraka da ya yi na kwanaki uku a kafar LoveWorld USA, faston mai shekaru 60 ya tabbatar da cewa cocinsa dawo da matattu sama da 50.

Wannan lamari mai ban mamaki dai ya faru ne daga ranar 15 zuwa 17 ga Maris, 2024, inda ya ja hankali da muhawara a duniya. Mun tada matattu sama da 50, inji fasto Chris

Wadanne irin mutane aka tayar daga mutuwa?

A bidiyon kai tsaye da aka yada a shafin Facebook na LoveWorld USA a ranar 17 ga Maris, fasto Oyakhilome ya bayyana cewa aikinsa na ‘tashin matattu’ ya kunshi tado da mutane daban-daban masu shekaru daban-daban.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, ya ce: “A cikin shekarar da ta gabata, mun sami sama da mutane 50 da muka yarar daga mutuwa, sama da mutane 50.

“Ta yaya za ka ba da bayanin irin wadannan abubuwan?
Manya da matasa, a kasashe daban-daban, ta yaya za ka yi bayani?” Wasu za su yi shakkun lamarin Sai dai, da kansa ya fadi cikin wasa cewa, akwai yiwuwar a yada kokonta da shakku kan wannan batu da ya yi na tada matattu.

Ba wannan ne karon farko da ake samun malamin addinin Kirista ya yi da’awar tada matattu ba, an sha yin hakan a kasar nan. Duk da haka, ana samun masu sharhi da nuna shakku kan lamarin, inda wasu ke ganin malaman na shirga karya ne kawai.

Related posts

Leave a Comment