Na Shiga Damuwa Dalilin Yawaitar Karuwai A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwarsa kan yadda karuwanci da ayyukan assha ke yawaita a cikin sansanin yan gudun hijra dake jihar Borno.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda wata tawagar kwamitin majalisar dattawa kan harkoki na musamman ta ziyarcesa karkashin jagorancin, Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, a Maiduguri.

A ranar Juma’a, rahoto ya bayyana cewa kwamitin majalisar da ta kunshi Sanatoci 12 sun tafi Borno domin duba ayyuka da nasarorin da hukumar cigaban Arewa maso gabas NEDC ta samu a Borno da sauran jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Rahotanni sun bayyana yadda ‘Yan Mata da wasu Mata musamman wadanda aka karkashe mazan su suka mayar da zinace zinace a matsayin wata hanya ta samun kuɗaɗen shiga.

Binciken baya bayan nan ya nuna cewar Sojoji da ke kula da sansanin da wasu Ma’aikatan agaji sune suka assasa wannan muguwar ɗabi’a ta lalata da Mata a sansanin ‘yan gudun hijira, inda ya zamana Matan ba su samun abincin da za su ci har sai sun amince an yi fasiƙanci da su.

A hannu guda kuma wasu Maza daga cikin garin Maiduguri suna ziyartan sansanin domin neman abokanan lalata, hakazalika rahotanni sun bayyana cewar har daga wasu jihohi makwabta ana zuwa sansanin na ‘yan gudun hijira domin sheƙe aya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply