Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Na Samu Kwarin Gwiwa A Lambar Yabon Da Kungiyar Likitocin Kashi Ta Bani – Farfesa Ahmad Rufa’i

Kwararren Likita ta ?angaren kula da ?ashi a Najeriya sannan babban Malami a jami’ar Gwamnatin tarayya dake Maiduguri babban birnin Jihar Borno Farfesa Adamu Ahmad Rufa’i, ya bayyana lambar yabo da kungiyar Likitocin ?ashi ta Najeriya suka bashi a matsayin wani abu da zai ?ara mishi karsashi ?angaren ayyukan sa.

Farfesa Ahmad Rufa’i ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna jim ka?an bayan kar?ar lambar yabon da kungiyar ta bashi.

“Lambar yabo irin wannan lamba ce ta musamman da sai an tantance mutum kafin a bashi ita, tantance ni da aka yi da za?oni cikin dubban mutane aka karramani hakan ya zaburar dani tare da ?ara mini ?warin gwiwa akan ayyukana musamman matsayina na Likitan ?ashi”.

Farfesa Rufa’i ya bayyana aikin likitanci musamman aikin likitan ?ashi a matsayin wani abu mai matukar tasiri, wanda hakan ya sanya lokacin da zai shiga jami’a bayan kammala karatun sakandare ya canza niyyarsa ta farko ta karatun aikin likita zuwa bangaren likitan ?ashi saboda muhimmancin sa da ?arancin mutanen mu a ciki.

Farfesan ya tabbatar da cewa babu Likitocin da ake wawarsu a fa?in duniya irin Likitocin ?ashi, saboda babu wani ?an Adam wanda bai da bu?ata zuwa ga likitan ?ashi, ?alibai da dama da ya karantar a yanzu haka suna kasashen waje suna gudanar da ayyukan su, shima dalilin da ya sa bai tsallaka ?etare ba kishin ?asa da yake dashi ne na ganin ya bada gudunmawa ga Najeriya.

Daga ?arshe Farfesa Adamu Ahmad Rufa’i ya yi kira ga dalibai musamman masu karantar likitanci ?angaren ?ashi da cewar su dage tare da bada himma sosai a wannan fanni domin muhimmancin haka ga rayuwar al’umma gaba ?aya.

Exit mobile version