Kwararren Likita ta ɓangaren kula da ƙashi a Najeriya sannan babban Malami a jami’ar Gwamnatin tarayya dake Maiduguri Jihar Borno Farfesa Adamu Ahmad Rufa’i, ya bayyana lambar yabo da kungiyar Likitocin ƙashi ta Najeriya suka bashi a matsayin wani abu da zai ƙara mishi karsashi ɓangaren ayyukan sa.
Farfesa Ahmad Rufa’i ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna jim kaɗan bayan karɓar lambar yabon da kungiyar ta bashi.
“Lambar yabo irin wannan lamba ce ta musamman da sai an tantance mutum kafin a bashi ita, tantance ni da aka yi da zaɓoni cikin dubban mutane aka karramani hakan ya zaburar dani tare da ƙara mini ƙwarin gwiwa akan ayyukana musamman matsayina na Likitan ƙashi”.
Farfesa Rufa’i ya bayyana aikin likitanci musamman aikin likitan ƙashi a matsayin wani abu mai matukar tasiri, wanda hakan ya sanya lokacin da zai shiga jami’a bayan kammala karatun sakandare ya canza niyyarsa ta farko ta karatun aikin likita zuwa bangaren likitan ƙashi saboda muhimmancin sa da ƙarancin mutanen mu a ciki.
Farfesan ya tabbatar da cewa babu Likitocin da ake wawarsu a faɗin duniya irin Likitocin ƙashi, saboda babu wani ɗan Adam wanda bai da buƙata zuwa ga likitan ƙashi, ɗalibai da dama da ya karantar a yanzu haka suna kasashen waje suna gudanar da ayyukan su, shima dalilin da ya sa bai tsallaka ƙetare ba kishin ƙasa da yake dashi ne na ganin ya bada gudunmawa ga Najeriya.
Daga ƙarshe Farfesa Adamu Ahmad Rufa’i ya yi kira ga dalibai musamman masu karantar likitanci ɓangaren ƙashi da cewar su dage tare da bada himma sosai a wannan fanni domin muhimmancin haka ga rayuwar al’umma gaba ɗaya.