Gwamnan jihar Borno, Babagana Umar Zulum, ya bayyana cewa akwai masu yiwa yaki da rikicin Boko Haram a Arewa maso gabas zagon kasa kuma ya kamata shugaban kasa ya san gaskiya.
Zulum ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin gwamnonin jam’iyyar APC karkashin jagorancin gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu.
Gwamnonin sun kawo masa ziyarar jaje bisa harin da aka kai masa a garin Baga, karamar hukumar Kukawa, ranar Laraba, 29 ga Yuli, 2020.
Yace: “Bari in sake jaddada matsayata da nayi a baya kan yaki da ta’addanci a Borno, ina mai jaddadawa kuma ko shakka babu, ba za’a iya hada rikicin a 2011 – 2015 da 2015 zuwa yanzu ba.”
“Shugaban kasa ya yi kokari, amma abu mai muhimmanci shine, yana da kyau a fadi abinda ya dace. Akwai masu zagon kasa da basu son rikicin ta’addancin nan ya kare.
Ya kamata shugaban kasa ya san wannan abin mai muhimmanci.”
“Yayinda ya zo Maiduguri watanni biyu da suka gabata, na fadi haka saboda tsakanin 2011 da 2015, kimanin kananan hukumomi 22 na karkashin yan ta’adda.” “Daga cikin manyan hanyoyin shiga Maiduguri hudu, guda daya kawai ke bude. Amma yanzu an samu canji.
Duk da haka, akwai abu guda daya da ya kamata mu mayar da hankali, shin meyasa yakin yaki karewa?” “Ina jaddada cewa akwai zagon kasa a lamarin nan, saboda haka, ya kamata shugaban kasa ya duba matsalar tsaron yankin nan don kawo karshenshi.”
A nasa bangaren, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, ya tabbatarwa gwamna Zulum cewa suna bayansa. “Mun zo Borno yau ne a madadin takwarorinmu don taya abokinmu, Gwamna Babagana Umara Zulum murnar Sallah. Na biyu kuma mu jajanta masa bisa abinda ya faru a Baga kwanakin da suka gabata.”
“Allah ya cigaba kareka da dukkan al’ummar jihar Borno, kuma Allah ya taimaka mana wajen yakan makiyan ciki da waje.”
A bangare guda, Gwamna Zulum ya bayyana takaicinsa kan yadda adadin masu zama a sansanin gudun hijra ke ƙaruwar, ya ce akwai bukatar mutane su koma gidajensu tun da an samu zaman lafiya.