Na Kori Sunusi Daga Sarauta Ne Saboda Rashin Cancanta – Ganduje

Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana manyan dalilan da suka sa shi ya tu?e Muhammadu Sunusi II daga karagar sarkin Kano, inda ya tabbatar da cewa tun asali Sunusi bai cancanta ya zama Sarki ba, kuma ba ?aramin zunubi aka aikata ba na dorashi Sarauta da aka yi.

Gwamnan ya bayyana tu?e sarkin a matsayin matakin gaggawa don ceto tsarin mulkin masarautar gargajiya daga kama-karya, da shiga garari ta jefa baragurbi a cikin ta.

Gwamna Ganduje ya yi wannan jawabi ne wajen bikin ?addamar da littafi da aka rubuta kan tsohon shugaban ?asa, Goodluck Jonathan, wanda shahararren dan jaridar nan, Bonaventure Philips Melah, ya rubuta.

A cewar Ganduje, Sunusi ba shine mutumin da tun farko ya cancanci hawa kujerar sarautar da aka na?a shi ba a watan Yunin 2014 ba, an nada shi ne don kunyata tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Idan ba’a manta ba, a watan Afrilu na shekarar 2014 ne shugaban kasa na wannan lokacin, Goodluck Jonathan, ya sauke Sunusi daga mu?amin sa na gwamnan babban bankin kasa (CBN) bayan ya yi zargin cewa dalar Amurka biliyan 49 ta yi batan dabo.

Ganduje ya soki lamirin kasassa?ar da tsohon Sarkin ya yi, inda ya bayyana cewa ya kamata ya tattauna maganar tare da shugaban ?asa a sirrance ne ba wai ya fito yana shela a duniya ba.

Kazalika, ya kuma yabawa Goodluck Jonathan a kan matakin da ya dauka na cire Sanusi a wancan lokacin tare da bayyana hakan a matsayin abinda ya dace.

Related posts

Leave a Comment