Shugaba Buhari ya bayyana damuwar sa kan yadda farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabi a fadin kasar.
Shugaba Buhari ya baiwa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa gwamnatinsa ta yi babban shiri na daidaita lamuran farashin kayan masarufi.
Gwamnatin Shugaba Buhari ta tattauna da manyan masu ruwa da tsaki a harkar abinci, da taimakonsu, za a rage farashin kayan abinci.
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa ta hanun babban hadiminsa ta fuskar watsa labarai, Malam Garba Shehu a ranar Laraba, ya nuna takaicinsa kan tashin farashin kayan abinci.
Ya yi nuni da cewa bai kamata ace farashin kayan abincin ya tashi a dai dai wannan lokaci dan tattalin arzikin kasar ke kokarin farfadowa ba, sakamakon annobar COVID-19.
Shugaban kasar ya ba ‘yan Nigeria tabbacin cewa karin farashin kayan abincin na gajeren lokaci ne kawai, sakamakon shirin da gwamnatinsa ta yi na dai daita lamura.
Bugu da kari, fannin noma zai mayar da hankali wajen samar da kayayyakin noma musamman taki, da zai taimaka wajen karya farashin abinci, da samar da aikin yi.