Na Amince Da Kayen Da Nasha A Kotu – Ahmed Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce ya amince da hukuncin kotu na tabbatar da Bashir Machina a matsayin dan takarar sanata na Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023 dake tafe.

A ranar Laraba, kotun tarayya ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta amince da Machina a matsayin halastaccen dan takarar APC na Yobe ta Arewa sannan ta yi fatali da sunan Ahmed Lawan.

A cikin sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Lawan ya ce bayan tuntunbar abokansa na siyasa, ya yanke shawarar ba zai daukaka kara ba zai hakura ya rungumi ƙaddara.

“A ranar Laraba, 28 ga watan Satumban 2022, babban kotun tarayya a Damaturu ta yanke hukunci kan halastaccen dan takarar sanatan Yobe ta Arewa. “Hukuncin ya ce ba ni ne halastace ba don haka shiga na zabe bai halasta ba. “Bayan tuntubar abokai na na siyasa, magoya baya da masu fatan alheri, na yanke shawarar ba zan daukaka kara ba. Na amince da hukuncin.” Zan cigaba da bada gudumawa ga al’ummar mazaba ta da Jihar Yobe.

“A wannan matakin, ina son mika godiya ta ga mai girma, Sanata Ibrahim Gaidam bisa jagorancinsa a APC a Jihar Yobe. Ina kuma gode wa mai girma Gwamna Mai Mala Buni bisa goyon baya da yan uwantaka. “Ga mazaba ta, ina muku godiya bisa goyon baya da tallafi a aikin mu na gina mutanen mu na mazabar Yobe ta Arewa da Jihar Yobe.

Labarai Makamanta

Leave a Reply