N-Power: Za Mu Biya Ragowar Masu Cin Gajiyar Shirin – Sadiya

Ministar Harkokin Agaji da Jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta amince a yi biya na ƙarshe ga ‘yan rukuni biyu na masu cin moriyar shirin tallafi na N-Power wanda ɗaya ne daga cikin shirye-shiyen gwamnati na agaza wa matasa.

Wata sanarwa da mai taimaka wa ministar kan yaɗa labarai, Madam Nneka Anibeze, ta rattaba wa hannu, ta bayyana cewa ministar ta bada umarnin ne a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2020.

A cewar ta, ministar ta bada umarnin a biya kuɗin ne ga masu cin moriyar shirin na N-Power a Rukunnan A da B.

Ta ce, “Har an miƙa takardar umarnin a yi biyan har zuwa na watan Yuni, 2020 na rukunnan biyu ga ofishin Akanta Janar na Tarayya (AGF) domin su yi tantancewar ƙarshe kuma su biya.

“Biyan da kawai ya rage, wanda ke jiyan a tura takardun zuwa ofishin Akanta-Janar na Tarayya, shi ne na watan Yuli na masu cin moriyar a Rukunin B,” inji ta.

Bugu da ƙari, ministar ta yi bayanin cewa masu cin moriyar shirin wajen mutum 14,000 waɗanda ofishin Akanta-Janar ya tsallake su a lokacin biyan watan Maris zuwa Yuni, 2020 za su iya kasancewa cikin waɗanda na’urar GIPMIS da ake biya da ita ta ƙi shigar da sunayen su saboda akasin bayanai da ta gani game da asusun su na banki kamar yadda ma’aikatar ta tura wa ofishin Akanta-Janar.

Ta nanata cewa rahoton da aka samu daga ofishin Akanta-Janar ya nuna cewar duk wanda ke samun biyan kuɗi daga wasu hukumomin gwamnati, na’urar biya da ake kira ‘Government Integrated Financial Management System’ (GIPMIS) ba za ta amince ta biya shi wannan kuɗin ba, za ta riƙe su.

Hajiya Sadiya ta bayyana cewa ta buƙaci ofishin Akanta-Janar ɗin ya turo mata sunayen waɗanda abin ya shafa tare da dalilin rashin biyan nasu, kuma ta yi alƙawarin za ta sanar da waɗanda abin ya shafa.

Ta ƙara da cewa idan an ƙi biyan su ne a bisa kuskure, to waɗanda abin ya shafi su sani cewa za a biya su dukkan kuɗin su da zaran ofishin Akanta-Janar ya gyara kuskuren da aka samu.

Har ila yau, ministar ta bayyana cewa Rukunnan A da B na masu cin gajiyar shirin na N-Power sun riga sun sani tun daga farko, tunda da dai an faɗa masu, cewa da ma wa’adin shirin na tsawon watanni 24 ne.

Ta ƙara da cewa rashin cire masu cin moriyar shirin na Rukunin A bayan sun cika watanni 24 ya faru ne saboda matsalolin da aka samu a lokacin.

Ta ce, “Saboda haka, waɗanda wa’adin su ya ƙare a Rukunin A bayan watanni 40 da Rukunin B bayan watanni 24 ya yi daidai da ƙa’idar da aka yi da su a lokacin da aka ɗauke su.

“Wannan ya yi daidai da abin da ya faru lokacin da aka dawo da shirin na N-Power a ƙarƙashin ma’aikatar a ƙarshen shekarar da ta gabata, wato babu wani tsari da aka yi masu na cewar za a ɗauke su aiki kai-tsaye a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kan su ko a saka su cikin wata harkar sana’a kafin a maida shirin a ƙarƙashin ma’aikatar.”

Ministar ta shawarci waɗanda wa’adin su ya zo ƙarshe a shirin da su ci gaba da haƙuri domin ta na wani ƙoƙari ta tuntuɓar hukumomin gwamnati daban-daban, ciki har da Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Ma’aikatar Aikin Gona da Inganta Karkara ta Tarayya don ganin yiwuwar sun shigar da waɗanda su ka ci moriyar shirin zuwa cikin wasu shirye-shirye na gwamnati ko ma a ba su aiki idan ya samu.

Ta ce: “Mun buƙaci ma’aikatan shirin da ke dukkan jihohi da su ba mu sunaye da cikakken bayani na waɗanda wa’adin su na cin moriyar shirin na N-Power ya cika waɗanda ke da ra’ayin shiga tsari na gaba na ma’aikatar mu.”

Hajiya Sadiya ta kuma bayyana cewa za a yi wa masu cin moriyar shirin a Rukunin C da za a fara da su nan gaba kaɗan cikakken bayani kan shigar su shirin da iyakar wa’adin sa a daidai lokacin shigar su, don kauce wa rashin fahimtar da ta faru game da ‘yan Rukunnan A da B.

Ta ƙara da cewa za a yi cikakken shiri tun kafin wa’adin zaman su cikin shirin ya cika don kauce wa abin da ke faruwa a yanzu.

Ta ce, “Za a yi aikin tantancewa sosai na waɗanda ke son su shiga shirin a Rukunin C don tabbatar da an zaɓi waɗanda su ka dace.

“Ma’aikatar za ta yi aikin tantancewar a bayyane ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba wajen zaɓen waɗanda su ka cancanta daga cikin mutane 5,000,000 (milyan biyar) da su ka cike takardun neman shiga shirin.

“An tsara shirin N-Power ne domin a taimaka wa matasa ‘yan Nijeriya ‘yan shekara tsakanin 18 zuwa 35 domin su samu ƙwarewar da za ta taimaki rayuwar su don su zama masu kawo sauyi a cikin al’ummar su kuma su kasance masu faɗa a ji a harkar kasuwanci a gida da waje, kuma za a riƙa ba su kuɗin agaji N30,000 a kowane wata.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply