N-Power: Matasan Da Muka Ɗauka Na Zambatar Shirin – Sadiya

Ministan jinkai da bada tallafi, Sadiyya Farouk ta shaida cewa akwai dayawa daga cikin masu amfana da N-Power, wato karbar Alawus duk wata, suna aiki a wasu wuraren, haka bincike ya nuna.

A takarda da ministan ta fidda ranar Alhamis, ta ce tabbas akwai wadanda ba abiya su ba amma kuma ba daga ofishinta bane aka samu wannan matsala, tuni ofishin ta ta mika sunayen mutum sama da 500,000 domin a tantance su a biyasu kudadaen su na baya.

Ta ce akwai tantance sunaye da ake tayi ne domin bankado masu zambatar hukumar, suna karbar kudade bayan suna aiki a wasu wurare.

” Wannan shiri na wadanda basu da aikin yi ne amma wasu dubbai cikin wadanda ke karbar alawus tuntuntuni ashe suna aiki a wasu wurare kuma suna karbar alawus din N-Power.

” Yanzu ana yin tankade da reraya ne domin gano su da wancakalr da su daga cikin wadandaza a biya.

Ta roki masu amfana da shirin da ba a biya su kudaden su na baya ba su kara hakuri cewa nan ba da dadewa ba za su ji alat.

‘Yan N-Power sun yi zanga-zangar dakatar dasu da minista Sadiya ta yi a Abuja

Daruruwan matasa da suka halarci taron gangami don yin zangazangar dakatar da su daga shirin tallafi na N-Power daga fadin kasar nan da aka yi a Abuja ranar Juma’a sun bayyana cewa lallai gurguwar shawara ce dakatar da matasa da gwamnati tayi.

Matasan sun yi tattaki har zuwa majalisar Kasa domin nuna rashin amincewar su da dakatar da shirin cikin kankanin lokaci.

Daya daga cikin wadanda suka halarci wannan gangami kuma wakili daga jihar Kano, a zantawa da yayi da wakilin mu, ya shaida cewa suna kira ne ga gwamnati da ta jinkirat wannan shawara ta ta, sannan ta biya wadanda har yanzu ba a biya su alawus dinsu na wata uku ba.

Sannan kuma sun yi kira da a basu kudin tallafi ganin cewa matasan sun dade suna amfana da wannan tallafi na gwamnati.

Bayan sun gana da wasu daga cikin ‘yan majalisa da suka saurari kukan sai kuma suka dunguma zuwa rukunin sashen ma’aikatan gwamnatin Tarayya, domin ko za su yi kicibus da ministan samanr da tallafi ta Kasa, Sadiya Farouk.

Fitaccen Mai Rajin Kare Hakkin dan Adam, Komared Mustapha Soron Dinki, da ya yi tattaki tun daga Kano zuwa Abuja tare da matasan ya ce wannan gangame an yi shi don tunasar da minista domin wadanda suke amfana da shirin da dama ba abiya su hakkokin su ba kafin a dakatar dasu.

” Tun safe matasa suka yi dandazo a majalisar Kasa. Muna fatan gwamnati zata ji kukan matasan nan a samar musu da mafita da zai taimaka musu wajen ci gaba da rayuwa kamar da.

Matasan rike Kwaleye dauke da rubutu na kira ga gwamnati su waiwaye su da idon rahama.

Labarai Makamanta

Leave a Reply