N-Power: Gwamnati Ta Ƙara Wa’adin Mako Biyu Ga Masu Sha’awa

Minista Sadiya Umar Faruk ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kara wa’adin Sati biyu ga masu bukatar shiga shirin gwamnatin tarayya na N-power.

Sadiya ta bayyana hakan ne a yau Litinin, bayan shafe kusan wata daya ana cike fom din neman aikin na N-power.

Sai dai ga wadanda suke cin gajiyar shirin a rakuni na farko da kuma rukuni na biyu suna ci gaba da neman a biya su albashin da suke bi na tsawon wata hudu zuwa biyar.

Idan dai ba’a manta ba a satin da ya gabata ma’aikatan na N-power sun gudanar da zanga-zanga don neman Gwamnati ta biya su bashin albashin da suke binta.

Sai dai zuwa wannan lokaci babu wata sanarwa ko bayani da ministan ta fitar gameda biyansu bashinda sukebi, dakuma batun tabbatar dasu a matsayin ma’aikata kamar yadda gwamnatin tarayya ta Alkawaranta a lokacin yakin neman zabe.

Ma’aikatan N-power sun bayyana takaicin yadda suka yi Sallah karama cikin yanayi na rashin kudi sakamakon rike musu albashin wata biyar da ministar ta yi, kuma sun nuna damuwa sosai kan hakan zai iya hana wasun su yin layya.

Akwai yiyuwar nan gaba kadan ma’aikatan na N-power za su shirya wata zanga-zanga da ba a san bunda za ta haifar ba.

Akwai al’ummomi da yawa dake neman gwamnatin tarayya ta kara yawan ma’aikatan da za ta dauka a rukuni na uku, kasancewar an samu ?utane masu dinbin yawa da suka nuna shawa’ar shiga cikin wannan shirin.

A bangaren Minista Sadiya kuma babu wani martani ko bayani game da wannan batun.

Labarai Makamanta

Leave a Reply