Fitacciyar Jarumar Fina-Finan Hausa Khadija Yobe wacce aka fi sani da Karima, a cikin fim din Izzar so. Ta bayyana harkar fim a matsayin hanyar fadakar da jama’a, da kuma sana’ar da ta ke samar da abin rufin asiri ga masu yin ta.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar ta da wakilin jaridar Dimokuradiyya, dangane da yadda a ke yi musu kallon mutanen da su ke bata tarbiyyar Matasa, in da ta ke cewa.
“To gaskiya ba haka ba ne, mutane ne su ke yi wa harkar mummunan zato, kuma shi mummunan zato haramun ne, don haka ya kamata mutane su rinka yi wa harkar fim adalci.”
Jarumar ta cigaba da cewar “Ni tun da na shiga harkar fim, babban buri na shi ne na zama ina fadakar da jama’a, ta hanyar isar da sakon da ya ke cikin fim, kuma ya zamar mun, wata sana’ar da za ta rufa mini asiri, don idan mutum ya kiyaye mutuncin sa, to zai ci ribar sana’ar fim, don haka na ke fatan na samu ribar da take cikin sana’ar fim din. ” Inji ta.
Da muka tambaye ta, dangane da yadda matan da su ka daukaka a fim, su ke ganin sun fi karfin aure kuwa, cewa ta yi.
” To ni ina ganin ba haka ba ne, domin shi aure lokaci ne, idan lokacin ya zo babu yadda za ka yi, kuma, don haka ni ina da burin ko me na ke yi idan Allah ya kawo mini miji nagari zan yi aure, wanda zai kare mun mutuncina, da na ya’yana, amma ni ba na kallon kudin mutum, ko wani abu da ya mallaka.” a cewar ta.