Musulmi Na Cikin Mawuyacin Hali A Najeriya – Sheikh Gwauron-Dutse

Babban malamin addinin musulunci a Kano Sheik Nasidi Abubakar Goron-Dutse ya koka a kan rayuwar kunci da yan Nijeriya ke ciki musamman musulmi.

Malamin, ya nuna damuwarsa a kan yadda wahalhalu, hauhawan farashin kaya da rashin aikin yi ke karuwa a kasar.

A cikin gajeren faifan bidiyon malamin da ya yi magana malamin ya ce wannan shine lokaci mafi muni da ya taba ganin musulmin Najeriya sun shiga.

A dukkan rayuwa ta, ban taba ganin musulmin Nijeriya cikin kunci wanda ya fi wannan ba.

Malamin ya cigaba da kira ga al’umma su taimakawa mabukata da masu karamin karfi komin kankantar abinda suke da shi inda ya ce, babu wani lokaci da jamaa sukafi bukatar taimako samada wannan.

Labarai Makamanta