Munin Mulkin Buhari Ya Fi Na Mulkin Mallaka – Omokri

IMG 20240308 WA0073

Shahararren dan gwagwarmayar zamantakewar al’umma, Reno Omokri, ya bayyana Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatinsa a matsayin abu mafi muni da ya afkawa Najeriya, Yana mai jaddada cewa tafi mulkin mallaka muni.

Reno Omokri yace Buhari yaci bashin kudi fiye da tsofaffin shugabannin Najeriya kamar Tafawa Balewa, Aguiyi Ironsi, Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Yar’Adua, da Goodluck Jonathan.

Ya koka da cewa duk da dimbin bashin da Buhari yaci, ya Kuma buga Takardun Naira “ba bisa ka’ida ba.”

A cewar Omokri: “Babban abin da ya taba faruwa a Najeriya shi ne Buhari. Buhari ya fi mulkin mallaka muni. Buhari yayi jagoranci maras manufa tsawon shekaru takwas. Yaci bashin kudi fiye da Tafawa Balewa, Ironsi, Gowon, Murtala, Obasanjo, Shagari, Babangida, Shonekan, Abacha, Abdulsalami, Yar’adua da Jonathan idan ka haɗe su waje Guda.

“Lokacin da Buhari ya zama shugaban kasa, Najeriya ta kasance mai kishi, Kuma Buhari ya kasance talaka. A yau, sabanin haka ne. Buhari ne a yanzu ya fi karfin kudi, Yayin da Najeriya ke fama da talauci. inji Reno Omokri

Labarai Makamanta

Leave a Reply