Munafukai Ne Kawai Ke Sukar Gwamnatin Buhari – Badaru

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar na jihar Jigawa, ya kwatanta masu kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari da masu gurbatacciyar zuciya da kuma rashin kishin kasa.

A yayin jawabi a taron mambobin APC na kafafen sada zumuntar zamani na yankin arewa maso yamma da aka yi a Dutse, gwamnan ya ce halin da tsaron kasar nan ke ciki ya gyaru. Ba a hada yanzu da lokacin da mayakan ta’addanci na Boko Haram ke kai wa jama’a hari a wuraren bauta, kasuwanni, tashoshin mota da sauran wurare ba.

Badaru ya kara da cewa, a yanayin ayyukan inganta rayuwa da gwamnatin Buhari ta yi, za a iya cewa ya cika alkawurran da ya daukarwa ‘yan Najeriya. Ya kalubanci ‘yan Najeriya da su fito su duba nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu, sannan a alakanta su da na gwamnatin da ta gabata.

Related posts

Leave a Comment