Muna Maraba Da Makiyaya A Jihar Borno – Zulum

Gwamnatin jihar Borno ?ar?ashin jagorancin Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ta ce za ta samar da wuraren kiwo ga makiyaya wadanda ke son kafa kasuwanci a jihar, domin inganta jin da?i da walwalar Makiyaya a yankin Arewa maso Gabas.

Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, ya ce jihar Borno na da filin noma mai fadin kusan kilomita murabba’in dubu 73 wanda zai iya daukar yawan dubban makiyaya a fa?in ?asar.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin a yayin kaddamar da fara aikin gaggawa na Hukumar Kula da Yankin Arewa-maso-Gabas a Maiduguri babban birnin Jihar ta Borno.

Zulum ya bayyana cewa, ya kasance yana goyon bayan samar da wuraren kiwon makiyaya a tsakanin jihohi shida na Arewa maso Gabas domin hakan bawai zai samar da ci gaban tattalin arziki ga yankin bane kawai, zai bunkasa har da jerin kayan amfanin gona na yankin.

“Muna da filayen noma a nan Arewa maso Gabas. Na dade ina ba da fatawar a kirkiro da wuraren kiwo a jihar. Kowace jiha a Arewa-maso-Gabas na iya samar da akalla hekta 5,000 na cibiyoyin kiwo inda za mu bunkasa kiwon dabbobi har miliyan biyu zuwa uku.”

Gwamnan ya ce yayin da wasu ke korar makiyaya daga jihohin su da yankin su, jihar Borno za ta nemi samar da filaye don kafa cibiyoyin da za su taimaka wajen samar da dabbobi da kuma bunkasa ayyukan noma a jihar.

Related posts

Leave a Comment