Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce ta yi maraba da hukuncin kotun ?olin ?asar wadda ta umarci gwamnonin su daina ri?e wa ?ananan hukumomi ku?a?ensu da ake ware musu daga asusun gwamnatin tarayya.
Shugaban ?ungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman ya ce ?ungiyarsu za ta yi biyayya ga hukuncin kotun, yana mai cewa a yanzu lauyoyinsu sun bu?aci kwafin hukuncin kotun wanda za yi nazari a kai.
Ya ?ara da cewa gwamnonin na murna da karkasa iko dangane da ‘yancin ?ananan hukumomin.
”Hakan zai rage wa gwamnoni nauyi, mutane ba su san yadda jihohi ke kashe ma?udan ku?i wajen ?aukar ?awainiyar ?ananan hukumomi ba ”, in shugaban ?ungiyar gwamnonin ?asar.
Da dama dai na ganin wannan hukunci zai shafi jihohin ?asar, musamman yadda suka saba ri?e ku?in ?anannan hukumomin da kuma ayyukan da suke yi.
To sai dai gwamnan na Kwara ya kare matakin da cewa hakan ba zai shafi jihohin ba, musamman jiharsa ta Kwara da ya ce dama ?ananan hukumomi na da ‘yanci, saboda dama a cewarsa ba ?arnatar da ku?in ?ananan hukumomin gwamnonin ke yi ba.
”Don haka yanzu sai ?ananan hukumomin su ci gaba da ri?e kansu, musamman a wannan lokaci da ake dab da tabbatar da mafi ?an?antar albashi, su tabbatar suna biyan albashin ma’aikata sannan sarakunan gargajiya su sami kashi 5 cikin 100 ku?in da ake bai wa ?aramar hukumar, wa?annan su ne manyan batutuwan”.
Wani ?angare na hukuncin shi ne haramta wa jihohin rusa za??a?un shugabannin ?ananan hukumomin.
Kan wannan batu shugaban ?ungiyar gwamnonin ya ce wannan zai shafi wasu gwamnonin, musamman wa?anda ba su da za?a??un shugabannin ?ananan hukumomin a yanzu.
A ranar Alhamis ne dai kotun kolin ?asar ta yanke hukuncin bayan da gwmanatin tarayya ta shigar da gwamnonin ?ara don su bai wa ?ananan hukumomin ‘yanci, bayan da aka zargi gwamnonin da ri?e ku?a?en nasu.