Muna Fata INEC Ta Dauki Darasi Daga Zaben Senegal – Atiku

IMG 20240316 WA0103

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya taya sabon za?a??en shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye murnar lashe za?en ?asar da aka yi a ranar 24 ga watan Maris ?in 2024.

Cikin wani sakon X da ya wallafa a yammacin Juma’a, Atiku ya ce nasarar gudanar da za?en lafiya ?alau, ya nuna akwai kyakkyawan fatan ?asashen da ke ?ar?ashin mulkin soji su ma za su iya komawa kan tsarin dimokra?iyya a nan gaba.

“A wajenmu Najeriya da wasu wuraren, akwai babban darasi da ya kamata mu koya a za?en Senegal

“Wannan yana ?ara tabbatar da cewa a ?ar?ashin dimokra?iyya ne ake iya samar da gwamnati mai inganci,” in ji Atiku.

Ya ce abin da aka gani a za?ukan Najeriya na 2019 da na 2023 sun nuna INEC ba ta yi abin da muka yi tsammani ba.

“Ina taya shugaban Faye murnar lashe za?e. Fatana shi ne za?en ya zama mai alfanu ga mutanen Senegal kuma ya zama zakaran gwajin dafi ga sauran ?asashen Yammacin Afrika.”

Related posts

Leave a Comment