Muna Duba Yiwuwar Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Gwamnonin Arewa

Gwamnonin Arewa maso Yamma suna duba yiwuwar yin sulhu da ‘yan bindiga da nufin kawo karshen kallubalen tsaro da ake fama da shi a yankin.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai wa takwararsa na jihar Zamfara, Bello Matawalle.

Hare haren ‘yan bindiga, satar shanu da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ta kazanta a jihohin Zamafara da Sokoto a baya bayan nan.

Yin sulhu da ‘yan bindigan ya haifar da sakamako mai kyau a cewar gwamnan Zamfara Bello Matawalle kamar yadda TVC News ta ruwaito. Akwai yiwuwar gwamnonin Arewa maso Yamma su dauki wannan matakin domin kawo karshen hare haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da satar shanu a yankin.

Tsohon gwamnan Zamfara, Mamuda Shinkafi ya yabawa kokarin da gwamna Matawalle ya yi na magance kallubalen tsaro a jihar. Ya yi imanin cewa sauya shugabannin hukumomin tsaro ba shine abinda ya fi dace wa ba a wannan lokacin da ake cikin tsaka mai wuya.

A wani labarin, a kalla mutum 20 ne suka riga mu gidan gaskiya kuma wasu da dama suka jikatta sakamakon sabbin hare haren da aka kai a wasu garuruwa uku a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ana zargin ‘yan daba ne suka kai harin da ya faru a ranar Alhamis kamar yadda Channels TV ta ruwaito. Garuruwan da aka kai harin sun hada da Kurmin Masara, Apyia Shyim, and Takmawai .

Wannan sabon harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan an tura jami’an tsaro zuwa wasu garruruwan da ake ganin sun cikin hatsari ko kuma rikici na iya barkewa. Sufeta Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tura jami’ansa domin kare rayuka da dukiyoyin mutanen garuruwan da abin ya shafa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply