Muna Dab Da Kawo Ƙarshen ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Katsina

A kokarinta na kawo karshen matsalar tsaro da wasu kananan hukumomin jihar Katsina, ke fama da ita, Kwararren masanin tsaro Kuma mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara kan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya ce wannan sabuwar hanya da muka bullo da ita za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da jihar ke ciki.

Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da RARIYA a ci gaba da shirye-shirye wani taron karawa juna sani da ofishin sa zai shiryawa manema labarai a ranar alhamis mai zuwa.

Gogaggen Masanin Tsaron, ya kara da cewa matsalar tsaro da muke fuskanta a jihar Katsina, tana bukatar nazari da bincike da kuma natsuwa. Idan aka rasa guda daga cikin wadannan ginshikai din yana da wahalar a kawo karshen ta. Saboda matsalar nan ba yau aka fara ta ba, kamar kansa ce kafin ta bayyana tana jikin dan Adam, lokacin da ta bayyana tana da wuya a magance lokaci daya. Gwamnati ta fara da binciken musassabin matsalar, bisa ga haka ne muke hadin-giwa da al’umma, shi yasa gwamna ya kai wata dokar sarakuna domin ayi Mata kwaskwarima ta a shigo da su don su ci gaba da bada guddumuwar kamar yadda suke a shekarun baya. Matsalar da muke fama da ita ta cikin gida ce, ba wai jami’an tsaro kadai ba ne za su kawo karshen ta ba. Bisa kokarin da al’umma ke yi to ya za’a yi a jawo al’umma ciki kuma tuni matakin ya fara haifar mana da da Mai ido, shi yasa kwanan nan hare-haren ma sun yi sauki kuma fahimtar ta fara daidaituwa.

Ibrahim Katsina ya ci gaba da cewa matakan da muka dauka na daidaita alammura na wadanda ke daji da wanda ake kaiwa hari za su zauna yadda za’a fahimci juna, an yi irin wannan a kasashen da suka cigaba. Yanzu haka yan bindigar sun fara gane muhimmancin zaman lafiya. Kura-kuran da muka yi a baya za mu gyara, akwai jahilci wajen su ya kamata malaman addinin musulunci suna da rawar da za su taka, kamar yadda ta faru a jihar Kaduna. Saboda jihilci ya fi kafirci illa. Haka zalika, turba ce ta tuntuba don ganin an yi wata manhaja mai dorewa, tsarin za’a sanya duk wani mai ruwa da tsaki ciki don ganin an bar zaluncin kowane bangare babu cuta babu cutarwa, a gwada kowa abinda yake bai dace ba, ba kudi zaa kashe ba, dabia ce ake gyarawa a wannan karon. Za mu zauna da malamai a tsara manhaja ta hanyar da’awa da wayar masu da kai.

Mai baiwa gwamna shawara ya ce tsari ne bisa ga yi wa kowa adalci da turbar addinin musulunci, bisa ga yafewa juna ba gwamnati za ta ce ta yafewa yan bindiga ba, su dai su nemi gafara al’umma da suke tare da su. Idan mun yi tsarin ba wai Katsina kawai ba, har sauran jihohi za su yi koyi bisa ga shimfida adalci. Ba za mu sa san rai ba, abinda muke so a yi mana kyakkyawa zato. Kofar mu a bude take na amsar korafe korafe da shawarwarin yadda za mu samu nasarar wannan aiki, harkar tsaro ta kowa ce kuma kowa na da guddumuwar da zai iya badawa.

Daga karshe, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana jin dadinsa bisa ga irin guddumuwar da al’ummar jihar Katsina ke badawa ta hanyar bada bayanan sirri ga Ofishinsa. Wannan fitina ta kusa zama tarihi a jihar Katsina ta hanyar tuntuba da adalci.

Labarai Makamanta