Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatar da cewar kwanan nan bada dadewa ba za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da ya da?e yana addabar Najeriya gaba ?aya, zaman lafiya ya namaye ko ina.
Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin taron bayar da bayani a kan ayyukan rundunar dakarun sojin Najeriya.
A cewarsa, yadda sojoji suke ragargazar ‘yan ta’adda, kwanan nan za su zama tarihi. Ya kara da cewa: “Rundunar Operation Hadarin Daji da sauran rundunoni masu taimakonsu suna ragargazar ‘yan ta’addan arewa maso yammacin kasar nan kuma suna samun nasarori na ban mamaki.
“Jaruman sojojin suna ratsa dazuzzuka, lungu da sako wurin neman ‘yan ta’adda a maboyarsu. “A ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, rundunar Operation Accord sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama har suka samo tarin bindigogi kirar AK47 masu yawa.
Sannan a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, rundunar ta je sintiri wuraren kauyen Gobirawa suka yi kacibus da ‘yan bindigan. A karon battar, sun kashe ‘yan bindiga 6, sannan suka samu bindigogi 2 kirar AK 47, kananun bindigogi 3 da babura 2.
“Sannan bayan rundunar sun yi amfani da dabara ta musamman, sun gano wasu mutane masu hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba guda 11. “Rundunar sun tura duk wadanda ake zargin ofishin ‘yan sanda don a cigaba da bincikarsu.