Muna Bukatar Karnuka Domin Yaki Da ‘Yan Kwaya A Najeriya – NDLEA

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a na ƙasa NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce, hukumar na bukatar karin kwararrun karnukan farauta da ke shinshino boyayyun kwayoyi.

Marwa ya bayyana cewa, farashin kowanne daya daga cikin karnukan ya kai Dala dubu 20, kwatankwacin Naira miliyan 18.

Koda yake bai yi karin haske ba kan adadin karnukan da yanzu haka hukumar ta NDLEA ta mallaka ba.

Marwa ya bayyana haka a gaban Kwamitin Majalisar Wakilan Kasar kan muggan kwayoyi domin kare kasafin kudin da aka ware wa hukumarsa ta NDLEA.

Marwa ya kara da cewa, a baya-bayan nan, gwamnatin Jamus ta bai wa NDLEA tallafin kwararrun karnuka, yayin da a gefe guda, kasar ta Jamus ke kan gina wata makarantar horas da karnuka ta kasashen Afrika ta yamma a birnin Lagos.

Ginin wannan makarantar zai lakume Euro miliyan 6 kamar yadda shugaban na NDLEA ya bayyana.

Matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi wani abu ne da ya daɗe yana ci wa Najeriya tuwo a kwarya, inda masana ke ganin tu’ammali da miyagun kwayoyi da matasa ke yi ya taimaka wajen jefa ƙasar cikin matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply