Muna Buƙatar SARS Ɗari Bisa Ɗari – Gwamnonin Arewa

Ƙungiyar Gwamnonin arewa 19 ta fito fili ta goyi bayan ayyukan Rundunar ‘yan sanda ta SARS, inda suka bayyana jin dadin ayyukan da SARS keyi a jihohin su, tare da yin Allah wadai da rusa rundunar da gwamnatin tarayya ta yi.

Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Filato Gwamna Simon Lalong ya sanar da manema labaran gidan gwamnatin hakan a jiya Alhamis.

Lalong ya sanar da hakan bayan wata ganawa da suka yi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan halin rashin tsaro da jiharsa ke fuskanta, har ya sanar da Shugaba Buhari akan NAFEST dake matsowa.

Gwamnan yace bai dace a rushe SARS ba, kamata yayi a gyara aikin nasu. tare da inganta shi baki daya.

A cewarsa, SARS na iyakar kokarinsu wurin yin ayyukansu yadda ya dace, saboda haka babban kuskure ne ɗaukar matakin rushe rundunar.

“Mu a matakan jihohin Arewa muna buƙatar rundunar SARS ɗari bisa ɗari, muna goyon bayan ayyukan su, mun yi tir da matakan gwamnatin tarayya na rusa su” lnji Shugaban Gwamnonin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply