Mun Yi Damarar Samun Nasarar Yakubu Lado A Takarar Gwamnan Katsina – Imrana Nas

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na yakin neman zaɓen Atiku/Lado na Jihar Katsina Alhaji Imrana Nas Shugaban Talakawa ya bayyana aniyar kwamitin nasu na ganin ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Yakubu Lado Ɗanmarke ya yi nasara a zaɓen dake tafe.

Imrana Nas ya bayyana hakan ne a yayin ganawar sa da manema labarai a Katsina jim kaɗan bayan ƙaddamar da kwamitin nasu da ya gudana a sakatariyar jam’iyar PDP dake Jíhar.

Shugaban kwamitin yaɗa labaran ya ƙara da cewar a fili yake jama’ar Jihar Katsina suna cikin wani mawuyacin hali na tagayyara wanda suke buƙatar ɗauki cikin gaggawa kuma tabbas Yakubu Lado shine mafita kasancewar shi gogaggen ɗan siyasa wanda ya fara tun daga matakin Kansila har ya zuwa Sanata.

Imrana Nas ya bayyana APC a matsayin matacciyar jam’iyya wadda ta mutu tuni shure-shure kawai take a yanzu bisa ga la’akari da yadda jama’a masu manufa suke ta ficewa daga cikinta zuwa PDP, mutane irin su tsohon sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mustapha Inuwa da sauran manyan ƙusoshin Jamiyyar.

Daga karshe Alhaji Imrana Nas ya yi kira ga jama’ar jihar Katsina da su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin samun nasarar PDP da ɗan takarar gwamnanta Alhaji Yakubu Lado a babban zaɓen dake tafe na shekarar 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply