Mun Watsar Da Sunayen Da Masarauta Ta Aiko Saboda Karɓar Rashawa – El Rufa’i

Gwamnatin jihar Kaduna ba za ta yi amfani da rahoton da majalisar nadin sarki na masarautar Zazzau ta kai mata ba domin cike gurbin sarkin Zazzau, biyo bayan zargin saye masu nadin Sarkin da gwamnatin El Rufa’i ta yi.

Gwamnan ya yanke wannan hukuncin ne bayan zargin da yayi an bai wa wasu daga cikin ‘yan majalisar cin hanci, kamar yadda ya wallafa a shafin sa tiwita.

A farkon makon nan ne aka bayyana cewa, ‘yan gidajen sarautu hudu ne daga gidaje uku na sarautar Zazzau suka fito neman kujerar. Sun hada da Iyan Zazzau, Bashir Aminu; Magajin Garin Zazzau, Ahmed Bamalli; Yeriman Zazzau, Munir Ja’afaru da Turakin Zazzau, Aminu Idris.

Daga cikin mutum hudun, ‘yan majalisar sun mika sunayen mutane uku inda Ahmed Bamalli bai samu shiga ba. Wata majiya daga fadar ta tabbatar da cewa, sunan Ahmed Bamalli bai shiga jerin bane saboda hatta kakansa bai yi sarautar Zazzau ba.

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi zargin cewa, daya daga cikin masu neman kujerar ya bai wa ‘yan majalisar cin hanci kafin su mika rahoton gaban gwamnan.

Hakan ce ta sa gwamnan ya yi kira ga dukkan masu neman karagar da su dawo a sake sabuwar tantancewa.

Jimillar masu neman kujerar sun kai mutum 11 kuma an samo sabuwar hanyar tantacewa wacce jami’an tsaro ce za su yi.

Labarai Makamanta