Mun Tura Sabbin Takardun Naira Bankuna – Gwamnan Babban Banki

Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, CBN, Godwin Emefiele, ya ce sabbin takardun kudi na Naira da aka canja wa fasali tuni sun isa bankuna kuma su na jiran a bada umarnin fara fitar da su.

A cewar wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafinsa na Twitter, Emefiele ya bayyana haka ne a Daura yayin da ya kai ziyarar yi wa shugaban kasa Muhanmadu Buhari karin bayani kan sake fasalin kudin Naira da kuma manufar hada-hadar kuɗi ta hanyar sadarwa da aka sake dawo da ita.

Ya ce sake fasalin kudin da kuma dawo da manufofin hada-hadar kudi ta hanyar sadarwa ba wai an yi ne don a cuzguna wa kowa ba, illa dai don ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Ya bukaci ƴan Najeriya da su rungumi hanyoyin sadarwa na zamani da ake amfani da su wajen hada-hadar banki da hada-hadar kudi a Najeriya.

“Sabbin takardun kudi na N200, N500, da N1,000 da aka sake fasalin yanzu suna nan a bankuna kuma a shirye suke don rabawa jama’a.

“Sake fasalin kudin da kuma sake bullo da manufofin hada-hadar kudi ta hanyar sadarwa ba wai don a taɓa wani ba ne sai don ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

“CBN ta jinkirta manufofin hada-hadar kuɗi ta hanyar sadarwa da yawa don shirya da zurfafa tsarin biyan kudin a Najeriya,” in ji shi.

Mista Emefiele ya shawarci ‘yan Najeriya da su kai tsohon takardun kudin su na N200, N500, da N1,000 zuwa bankuna kafin ranar 31 ga watan Junairu, 2023.

Babban bankin ya bayyana shirin sake fasalin wasu nau’ukan darajar Naira a yayin taron kwamitin sa na manufofin kudi, MPC, a ranar 26 ga Oktoba.

Don haka, ta sanya ranar 15 ga watan Disamba a matsayin ranar da za a fara buga sabbin takardun kudin Naira a hukumance, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar a ranar 23 ga watan Nuwamba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply