Mun Sauya Takardun Naira Domin Karya Wadanda Suka Tara Kudin Haram Ne – Buhari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da ‘yan ?asar cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan ?asar ba su wahala ba ta fuskar kasuwancinsu, da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofiin takardun ku?insu da sabbi a yayin da wa’adin da babban bankin ?asar ya saka ke ?ara ?aratowa.

Yayin da yake martani game da rahotonni dogayen layukan mutanen da ke shafe sa’o’i domin samun musanya tsoffin ku?insu a bankuna, lamarin da ya janyo suka daga ?angarorin adawa a ?asar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ?asar Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya jaddada cewa an fito da batun sauya fasalin ku?in ?asar ne domin yin maganin mutanen da suka ?oye ku?in haram, ba don cutar da talaka ba.

Ya kuma ce hakan zai magance matsalar cin hanci da rashawa da ?aukar nauyin ta’addanci da satar mutane domin kar?ar ku?in fansa.

Shugaba Buhari ya kuma ce tsarin zai taimaka wajen ?arfafa tattalin arzikin ?asar

Game da wahalhalun da talakawa ke sha na musanya ku?a?ensu kuwa, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi iya bakin ?o?arinta domin taimaka musu wajen musanya ku?a?ensu.

Ya kuma jaddada cewa babban bankin ?asar da sauran bankunan ?asar sun ?ara ha?aka hanyoyin musanya wa mutane ku?a?ensu domin tabbatar da cewa an musanya wa kowa ku?insa kafin cikar wa’adin.

Babban bankin ?asar dai ya saka ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar ?arshe ta daina amfani da tsoffin takardun ku?i na 200 da 500 da kuma 1000 a fa?in ?asar.

Related posts

Leave a Comment