Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya tayi nasarar daure mutane 2, 847 da suka aikata laifuffukan damfara a shekarar bana.
Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa ya yi wannan bayani yayin da bayyana a gaban majalisar ?asa bada rahoton ayyukan hukumar.
Abdulrasheed Bawa ya zauna da kwamitin yaki da rashin gaskiya na majalisar dattawa domin ya kare kasafin kudin hukumar na shekarar 2022/23.
An yi wannan zama ne a bayan labule, sai bayan nan Bawa ya samu lokaci ya zanta da ‘yan jarida. A cikin mutane kusan 3, 000 da aka yankewa hukunci a shekarar nan, Bawa yace mafi yawancinsu matasa ne da ya kamata su marawa hukumar baya.
Shugaban na EFCC yace masu danyen aikin su na bata sunan Najeriya a idon Duniya, yace doka ta ba su dama su yaki damfara da masu zamba cikin aminci.
“Ina kira gare su da su daina yin wadannan aika-aika a irin wannan gabar lokaci da kasar nan ta ke ciki. Ana shirye-shiryen zabe, gwamnati tana bakin kokari na ganin tattalin arzikin Najeriya ya dawo daidai.”