Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Mun Samar Da Sabuwar Arewacin Najeriya Ne Domin Magance Matsalolin Dake Addabar Yankin – Pastor Dara

An bayyana Jahilci da talauci a matsayin manyan ababen dake addabar yankin Arewacin Najeriya kuma ya zama silar jefa yankin cikin halin da yake ciki na ta?ar?arewar tsaro inda ya zamana koma baya a tsakanin sauran yankunan dake ?asar.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar ceto yankin Arewacin Najeriya, mai suna Pastor John Dara, lokacin wata tattaunawa da Gidan Talabijin da Rediyo na Liberty Abuja ya yi dashi a cikin shiri na musamman mai suna “Dialogue” a ?arshen mako.

Pastor Dara wanda ya kasance tsohon ?an takarar Shugabancin Najeriya ne a karkashin jam’iyyar NTP a shekarar 2011 ya kara da cewar, matsalolin da Arewa ke fuskanta da?a??u ne, wanda suka samo asali tun zamanin mulkin Turawan mulki zamanin Gwamna Lugga, hakazalika lokacin mai girma Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya yi kokarin shi na ganin ya shawo kan matsalar Arewa da ?o?arin daidaita yankin da sauran sashin ?asar, amma abin takaici bayan rasuwar shi wa?anda suka biyo baya sun gaza wajen ?ori akan abin da Sardauna ya yi, wanda hakan ya taimaka wajen sake mayar da yankin Arewa baya.

“Wannan yana daga cikin hikimar da ta sanya muka samar da wannan kungiyar wadda muka kira da sunan Sabuwar Arewacin Najeriya, muna da kyakkyawan yakini akan cewa abubuwa zasu daidaita muddin an bi hanyoyin da suka dace, ta hanyar amfani da Sarakuna da Malaman addini dake yankin, da gudummuwar sauran jama’a”.

Pastor John Dara ya ?ara da cewar a duk lokacin da al’umma suka wayi gari a cikin yanayi na rashin adalci babu shakka za’a ga ba daidai ba, inda ya bada misali da bullar kungiyoyin ta’addanci a yankin kamar Boko Haram da sauransu inda ya alakanta dalilin samuwar su dangane da rashin adalci da son zuciya, kuma babu shakka muddin ba a ?auki darasin gyara da yin adalci ba, abubuwa zasu cigaba da tafiya a rincabe ne.

” Munga illar da jahilci ya haifar mana a yankin Arewa, inda tarin yaran da basu samu damar halartar Makaranta ba, suka zame mana fitina wajen tayar da ?ayar baya da rusa kyakkyawan tarihin da aka san yankin da shi.

Exit mobile version