An bayyana Jahilci da talauci a matsayin manyan ababen dake addabar yankin Arewacin Najeriya kuma ya zama silar jefa yankin cikin halin da yake ciki na taɓarɓarewar tsaro inda ya zamana koma baya a tsakanin sauran yankunan dake ƙasar.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar ceto yankin Arewacin Najeriya, mai suna Pastor John Dara, lokacin wata tattaunawa da Gidan Talabijin da Rediyo na Liberty Abuja ya yi dashi a cikin shiri na musamman mai suna “Dialogue” a Ƙarshen mako.
Pastor Dara wanda ya kasance tsohon ɗan takarar Shugabancin Najeriya ne a karkashin jam’iyyar NTP a shekarar 2011 ya kara da cewar, matsalolin da Arewa ke fuskanta daɗaɗɗu ne, wanda suka samo asali tun zamanin mulkin Turawan mulki zamanin Gwamna Lugga, hakazalika lokacin mai girma Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya yi kokarin shi na ganin ya shawo kan matsalar Arewa da ƙoƙarin daidaita yankin da sauran sashin ƙasar, amma abin takaici bayan rasuwar shi waɗanda suka biyo baya sun gaza wajen ɗori akan abin da Sardauna ya yi, wanda hakan ya taimaka wajen sake mayar da yankin Arewa baya.
“Wannan yana daga cikin hikimar da ta sanya muka samar da wannan kungiyar wadda muka kira da sunan Sabuwar Arewacin Najeriya, muna da kyakkyawan yakini akan cewa abubuwa zasu daidaita muddin an bi hanyoyin da suka dace, ta hanyar amfani da Sarakuna da Malaman addini dake yankin, da gudummuwar sauran jama’a”.
Pastor John Dara ya ƙara da cewar a duk lokacin da al’umma suka wayi gari a cikin yanayi na rashin adalci babu shakka za’a ga ba daidai ba, inda ya bada misali da bullar kungiyoyin ta’addanci a yankin kamar Boko Haram da sauransu inda ya alakanta dalilin samuwar su dangane da rashin adalci da son zuciya, kuma babu shakka muddin ba a ɗauki darasin gyara da yin adalci ba, abubuwa zasu cigaba da tafiya a rincabe ne.
” Munga illar da jahilci ya haifar mana a yankin Arewa, inda tarin yaran da basu samu damar halartar Makaranta ba, suka zame mana fitina wajen tayar da ƙayar baya da rusa kyakkyawan tarihin da aka san yankin da shi.