Mun Kashe Biliyan 75 Wajen Buga Takardun Kudi A 2019 – Bankin Najeriya

Babban bankin Najeriya CBN ya ce ya kashe bilyan 75 wajen buga takardun kudade a shekarar 2019 kadai. Karin bilyan 11.5 kan abinda aka kashe a shekarar 2018.

Babban bankin ya kara da cewa an baiwa ‘yan kasuwan canji da hukumomin Hajji da Umrah $3.95 billion, kuma a matsayin alawus na tafiye-tafiye ga ma’aikatun gwamnati a shekarar.

Bayan haka, CBN ya bayyana cewa an samu ragin milyan N365.5 na kudin da mutane ke ajiye wa a banki. Dukka wannan ya bayyana ne a rahoton shekara-shekara da bankin ya saki na shekarar 2019.

Rahoton yace: “Jimillan kudin da aka kashe wajen buga takardun kudi a 2019 shine N75.5 billion, sabanin N64 billion a 2018, hakan na nuna cewa an samu karin bilyan 11.5.”
“An sayi kudin dala $3.95 billion a 2019, yayinda aka tura $2.58 billion jihar Legas, an bada $1.38bn ga Abuja da sauran jihohi.” “An yi amfani da kudin ne wajen ba ‘yan kasuwan canji da hukumomin Hajji, hakazalika wajen biyan kudin alawus na tafiye-tafiye ga ministoci, da manyan jami’an gwamnati.”

A bangare guda, Darakta Manaja na kamfanin Financial Derivatives, Bismarck Rewane, ya ce tattalin arzikin Najeriya zai durkushe nan da watanni masu zuwa a rubi’in kusa da karshen shekarar 2020.

Rewane ya bayyana hakan ga wakilan The Punch a ranar Talata inda yayi tsokaci kan Alkaluman da hukumar lissafin Najeriya NBS ta saki kan yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Rewane ya ce durkushewar tattalin arzikin Najeriya na nufin cewa za’a samu karuwan rashin aiki yi. Bayan haka, ya kara da cewa za’a ga yawan mutanen da zasu fada bakin talauci saboda karancin kudin da rashin aikin yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply