Mun Inganta Makarantun Allo A Jihar Kano – Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kafa makarantun Tsangaya uku a jihar domin gwamutsa karatun almajiranci da na boko a jihar, yadda za’a yaye Almajirai masu manufa nan gaba a fa?in Jihar ta Kano.

Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya sanar da hakan yayin rabar da kayayyakin koyarwa da kaddamar da jaridar “Teen Trust” a gidan Gwamnatin Kano a ranar Talata.

Ya ce an kafa makarantun ne bayan gwamnatin jihar ta haramta almajiranci ta kuma mayar da almajiran da ke jihar zuwa jihohinsu na ainihi. “An gina makarantun tsangaya uku domin almajiran jihar Kano da wadanda aka dawo mana da su daga wasu jihohin.

“Kawo yanzu mun zabi almajirai 100 domin su shiga makarantun, mun samar musu da kayayyakin karatu da tufafin makaranta,” in ji shi.

Ganduje ya ce gwamnatin jihar za ta cigaba da bada ilimi kyauta a jihar tare da shigar da makarantun almajirai cikin makarantun zamani domin bawa yara damar samun ilmin addini da na boko a lokaci guda.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin wasu malaman Firamare wadanda ba su da shaidar karatun malanta na NCE su tafi su yi karatun domin inganta aikinsu.

Related posts

Leave a Comment