Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana ainahin dalilan da suka sa ya dakatar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara daga yin wa’azi da kuma bayar da umurnin rufe masallacinsa a Kano, tare da yin watsi da ikirarin malamin na cewa lamarin siyasa ce.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta bari mutum daya ya jawo rashin zaman lafiya ba a jihar.
A zantawarshi da sashin Hausa na BBC a yammacin ranar Alhamis , Gwamna Ganduje ya ce: “Muna ta kallon ayyukansa a tsanaki. Jami’an tsaro na taka-tsantsan da abunda yake yi sosai kuma kafin daga bisani muka dauki mataki.”
“Ba za mu saurara wa kowa ba, duba da cewa abinda ya aikata zai iya kawo rashin zaman lafiya a Kano. Don haka jami’an tsaro na aikinsu don tabbatar da ci gaban zaman lafiya a Kano kuma ina fatan mutane za su fahimci hakan.”
Kan dalilin da yasa gwamnati bata saurari ta bakin Kabara don yin sulhu ba, gwamnan ya ce: “Ta yaya gwamnati zata watsar da shi? Bari na fada maku shi mayaudari ne, ta yaya gwamnati ta shiga wannan batu? Lokacin da ya shagala da cin mutunci da zagin malamai, shin gwamnati ce ta ce ya aikata hakan?
“Dalilin da yasa gwamnati ta shiga lamarin saboda yace duk mutumin da ya tunkari wajensa a yanka shi.”
Gwamna Ganduje ya ce hukuncin da gwamnatinsa ta dauka baya da nasaba da siyasa, inda ya kalubalanci malamin da ya ja da shi idan ya shirya. “Karya yake yi cewa hukuncin na da nasaba da siyasa.
Cewa yana umurtan mutanensa da su je suyi rijista, su je su yi. Akwai filin daga na siyasa, ya zo ya kara da ni ya ga abunda zai faru.
“Saboda ya tara wasu mutane suna tafa masa a koda yaushe sai hakan na sa shi takamar cewa yana da mutane.
Muma muna yin rijista a yanzu, bari mu ga wa zai yi nasara. Ai koda yaushe Allah na bayan masu gaskiya ne.”
Da yake martani ga ikirarin malamin na cewa kwamishinan ilimi na jihar ya gabbatar da cewa a tauye masa hakkinsa, Ganduje ya kalubalance shi da ya kawo hujjar cewa kwamishinan ya fadi abu makamancin wannan. “Muna so ya kawo faifan murya inda kwamishinan ya fadi hakan idan ba karya yake yi ba.
Abu na biyu mun ga bidiyo inda yace duk wanda ya je wurinsa a yanka shi. Wannan abu ne da ka iya kawo rikici kuma gwamnatin jihar Kano ba za ta bari hakan ya ci gaba ba.”
A baya mun ji cewa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi magana a kan dalilin da yake ganin shine ya sa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shi daga yin wa’azi.
A tattaunawarsa da jaridar Daily Trust bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya dauki wannan matakin a kansa, Sheikh Kabara ya yi zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa ba wai addini ba.