Mun Gaza Wajen Sauke Nauyin Matasa Dake Rataye A Wuyan Mu – Ministar Ku?i

“Mun gaza ta?uka komai wa ?a?anmu, mun kasa wajen sauke nauyin matasan Najeriya dake rataye a wuyan mu, duk martabobin da muke dasu a baya babu su a yanzu.
“Ya kamata mu tunatar da kanmu cewa akwai bukatar yaranmu su kasance a mi?e sannan cewa wannan ta’asar da ke gudana, a Najeriya ba za ta amfane su ba kuma ba zata amfani kasa ba”

Kalaman ministar ku?i Hajiya Zainab Ahmed kenan a yayin taron masu ruwa da tsaki da Matasa gami da masu ri?e da sarautun gargajiya da Malaman addini wanda ya gudana a Kaduna.

Ministar Ma’aikatar kudin ta bukaci iyaye da su cusa wa ?a?ansu akidar sanin martabobinsu, a matsayin wata hanya ta kare Najeriya daga dur?ushewa.

Ministar ta yi kiran ne a ranar Asabar, a garin Kaduna a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da hakimai 77, Shugabannin addinai da na gari daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Ministar ta kuma yi godiya bisa kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi wajen kula da lamarin tsaro.

Zainab Ahmed ta fada ma masu ruwa da tsakin cewa gwamnatin tarayya ta samar da wani shirin tallafawa matasa na naira biliyan 75. Ta ce an samar da shirin ne domin ba matasa a kasar damar habbaka kasuwancinsu da kuma dogaro da kai.

Ministar ta yi bayanin cewa kudin zai tallafa wa matasan wajen sanin hazikancinsu da tunaninsu kan kasuwanci, zama masu amfani da kuma daukar wasu aiki.

Da yake magana a wajen taron, ministan muhalli, Dr. Muhammad Mahmud, ya yi kira ga samun hadin kai wajen magance matsalolin tsaro a kasar.

Related posts

Leave a Comment