Mun Gano Dalilin Da Ya Sa ‘Yan Bindiga Ke Kashe ?alibai – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin kaduna ?arkashin jagorancin Gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i tayi Allah wadai da kisan wasu ?alibai dake karatu a manyan makarantun gaba da sakandire da yan bindiga keyi a jihar, tare da bada tabbacin da?ile faruwar hakan anan gaba.

A wani jawabi da kakakin gwamnan jihar, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata, ya jajantawa iyalan da abun ya shafa, tare da mi?a ta’aziyar gwamnati garesu. “Wannan kisan matasan da masu garkuwa da mutanen keyi wani ?angarene na ?o?arin su yaudari gwamnati.” “Kuma suna aikata wannan mummunan ta’addancin ne domin su saka gwamnatin Kaduna ta canza matsayarta daga ‘Ba biyan kudin fansa, ba tattaunawa’ zuwa yadda suke so.”

Muyiwa Adekeye ya kuma mai da martani kan wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ?auke da wata tattaunawa da aka yi da gwamna Malam Nasiru Elrufa’i tun shekarar 2014 yana ?alubalantar tsohon Shugaban kasa Jonathan. Inda ya yi watsi da wa?anda ke zargin gwamnan bisa matsayar da ya ?auka a kan matsalar sace-sacen mutane a jihar.

A cikin bidiyon, Anga gwamnan jihar Kaduna na kira ga gwamnatin tsohon shugaban ?asa Goodluck Jonathan, tayi amfani da duk wata dama, koda tattaunawa ce wajen ku?utar da yan Matan Chibok da aka sace.

Yayin da yake kare maganar gwamnan, Adekeye yace: “Tun daga wancan lokacin da lamarin Chibok ya faru zuwa yanzun, ya nuna cewa matakin da yafi dacewa a ?auka kan irin wa?annan sace-sacen shine ta hanyar amfani da ?arfi, wanda hukumomin tsaron mu suke yi a halin yanzu.

Related posts

Leave a Comment