Mun Dukufa Wajen Shawo Kan Matsalar Tsadar Abinci – Fadar Shugaban Kasa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta duƙufa kan ƙoƙarin magance tsadar farashin abinci a ƙasar.

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake buɗe taron bita kan ayyukan ministocinsa karo na uku don tantance irin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da ƙudurorin da gwamnatinsa ke bai wa fifiko.

“Muna yin gagarumin ƙoƙari don warware matsalar tashin farashin abinci mai alaƙa da hauhawar farashin da ake fama da shi a faɗin duniya.”

Alƙaluman baya-bayan nan, in ji shi daga Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar farashin ƙasar ta kai kashi 20.77 a watan Satumba.

Hukumar ta ce hauhawar farashin abiinci ya ƙaru ne sakamakon ƙaruwar farashin burodi da hatsi da sauran kayan abinci irinsu dankalin turawa da doya da man girki.

A yayin taron, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan raya ƙasa masu gagarumin tasiri a faɗin ƙasar, don haka shugabancinsa ya cimma muradai da burukan ‘yan Najeriya.

Ya nanata irin ci gaban da aka samu a fannoni kamar aikin gona da tattalin arziƙi da samar da ababen more rayuwa da tsaro da kula da lafiya da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply