Mun Ceto Dukkanin Daliban Kuriga 137 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Dajin Zamfara – Soji

IMG 20240308 WA0095

Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta kuɓutar da ɗalibai 137 na makarantar gwamnati ta Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Darektan da ke kula da harkokin yaɗa labarai na tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba a cikin wata sanarwa, ya ce sun ceto ɗaliban su 137 a dajin Zamfara.

A cewar sanarwar, sojojin sun ceto ɗalibai mata 76 da kuma maza su 61.

Tun a ranar 7 ga watan Maris ne aka sace ɗaliban firamare da na sakandare a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Kaduna kuma wani malamin makarantar da ya sha da ƙyar ya ce ɗalibai kusan 287 aka sace.

Malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi ya ce an sace ɗalibai na ɓangaren sakandare 187, sai kuma bangaren firamare ɗalibai 100.

“Sojoji tare da jami’an ƙaramar hukuma da na cibiyoyin gwamnati sun haɗa hannu wajen ceto ɗaliban da aka sace a makarantarsu da ke Kuriga,” in ji Edward Buba.

Sai dai mai magana da yawun shugaban Najeriya, Abdulazeez Abdulazeez ya shaidawa BBC Hausa cewa “ɗaya daga cikin malaman da aka sace tare da ɗaliban ya rasu”.

Tun da farko ƴanbindigar sun buƙaci a basu naira biliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa kafin ranar 27 ga watan Maris domin su saki ɗaliban. Kuma babu tabbas ko an biya kuɗin fansa kafin kuɓutar da ɗaliban.

Labarai Makamanta

Leave a Reply