Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS tace ta bankaɗo wani shiri da wasu manya a ƙasar nan suke yi na ganin sun tarwatsa Najeriya.
A cikin wata takarda da jami’in hulda da jama’a na Hukumar Peter Afunanya ya sanya wa hannu kuma aka rarraba ta ga manema labarai, yace sun gano shirin manyan ne na ƙoƙarin jefa gaba ta ƙabilanci da bambancin addini tsakanin jama’ar Najeriya, domin cimma manufar su ta tarwatsa ƙasar baki daya.
Rundunar ta ƙara da cewar ‘yan sandan farin kaya da sauran ƙwararru na rundunar na iya bakin kokarin su domin ganin haƙar mutanen bata kai ga ruwa ba.
“Lallai bayanan sirri sun zo mana akan aniyar waɗannan mutane da waɗanda ke ɗaukar nauyin su akan aika-aikar ta su, kuma ko kaɗan hukumar mu ba zata lamunci duk wani shiri da zai haifar da rudani gami da kawo tashin hankali a Najeriya ba.
Sanarwar ta buƙaci jama’ar Najeriya masu kishi da su taimaka wa hukumar tasu da bayanai na sirri da kai rahoton dukkanin wani gungun jama’ar da basu amince da su ba.