An bayyana wahala da jin jiki da Talakawa ke sha karkashin mulkin Shugaban Ƙasa Tinubu da cewar somin taɓi ce domin an jima da ankarar dasu masifar da za su fada amma suka yi biris.
Sanannen Ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahdi Shehu ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi da wakilinmu a Kaduna.
Mahdi Shehu wanda fitacccen magoyin baya ne ga ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a zaɓen da ya gabata, yace talakawa dai sun ci taliyar karshe a wannan mulki saura kuma a hari gaba.
Dangane da batun shari’ar Atiku da Tinubu da yanzu ke gaban kotu kuwa Mahdi Shehu ya tabbatar Atiku zai yi nasara sai dai ya gargadi Alkalai da cewar su sani cewa duk iya shari’ar ka da akwai wanda ya fika kuma yana jira a madakata.