Mulkin Tinubu: Najeriya Ta Talauce Amma ‘Yan Siyasa Na Fantamawa – Soludo

IMG 20240614 WA0052(1)

Da yake jawabi a wajen wani taro da ‘The Covenant Nation’ ta shirya domin saukaka ci gaban kasa, Soludo ya koka da cewa al’ummar kasar su na cikin wahala amma gwamnati da ?an siyasa na ci gaba da rayuwar fantama wa da yin rayuwar ?arya da hakkin talakawan da su ka za?e su.

Gwamnan ya ce a matsayin hanyar dakile rikicin da ke tasowa kada ya ta’azzara, ya kamata a sanya masu rike da mukaman siyasa a kan mafi karancin albashi na kasa.

Soludo ya bayyana cewa ?an Najeriya na fama da yunwa, karayar arziki da kuma talauci, amma masu mulki na ci gaba da rayuwa cikin almubazzaranci da cin mutuncin talakawa.

Yayin da ya ke kira da a kawo karshen almubazzaranci da kashe kudade a harkokin mulki, Soludo ya jaddada cewa dole ne a ko da yaushe zababbun jami’an su tuna cewa suna kan mukaman ne bisa amincewar jama’a.

Related posts

Leave a Comment