Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mai girma Shugaban ?asa Tinubu ya bayyana tsarin mulkin Dumukaradiyya a matsayin tsarin da ya fi kowane irin tsarin mulki a fa?in duniya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani ?angare na jawabin da ya gabatar a bikin ranar Dimokuradiyya ta bana a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Tinubu ya ?ara da cewa mulkin dimukuradiyya ne kacal a duniya ya ba jama’a damar za?en wanda suke so ya jagorance su bisa ga yarjejeniya ko al?awurran da aka yi a yayin ya?in neman za?e.
Kalaman Shugaban na matsayin martani ne ga gungun wasu jama’a da kungiyoyin wa?anda ke ganin babu wata riba ko nasara da mulkin dimukuradiyya ya samar, kuma har suke kiran cewa sojoji su dawo bisa madafun iko.