Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mai girma Shugaban ƙasa Tinubu ya bayyana tsarin mulkin Dumukaradiyya a matsayin tsarin da ya fi kowane irin tsarin mulki a faɗin duniya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani ɓangare na jawabin da ya gabatar a bikin ranar Dimokuradiyya ta bana a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Tinubu ya ƙara da cewa mulkin dimukuradiyya ne kacal a duniya ya ba jama’a damar zaɓen wanda suke so ya jagorance su bisa ga yarjejeniya ko alƙawurran da aka yi a yayin yaƙin neman zaɓe.
Kalaman Shugaban na matsayin martani ne ga gungun wasu jama’a da kungiyoyin waɗanda ke ganin babu wata riba ko nasara da mulkin dimukuradiyya ya samar, kuma har suke kiran cewa sojoji su dawo bisa madafun iko.