Mulkin Buhari: ‘Yan Adawa Ne Kaɗai Ke Faɗin Gazawar Shi – Matasan Arewa

Kungiyar cigaban matasan Arewacin Najeriya “Arewa Youth Colliation” ta yi kira ga jam’iyyun adawa su kyale shugaban ƙasa ya cigaba da ayyukan raya kasa, ba ƙoƙarin mayar da hannun agogo baya ba.

Shugaban kungiyar Matasan Kwamared Mukhtar Muhammad ya yi wannan kiran a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Kaduna.

Matasan sun kara da cewar ko shakka babu Buhari ya yi rawar gani a shugabancin kasar, domin lokacin da ya karbi mulki kasar na dab da tarwatsewa ne.

Matasan na Arewa sun yi kuma tir da matakan da kungiyoyin kudancin Najeriya ke dauka yankin Yarbawa da Inyamurai na barazanar ɓallewa daga kasar, inda suka ce dukkanin wadannan abubuwa na faruwa ne da nufin haifar da rikici a zaɓukan da ke tafe na shekarar 2023.

Matasan sun tabbatar da cewa Buhari ya yi ayyuka da dama na raya ƙasa idan aka kwatanta da shugabannin baya, kuma hakika ‘yan Najeriya zasu gane muhimmancin Buhari nan gaba bayan barin da shi Mulki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply