Mulkin Buhari: Najeriya Ta Kama Hanyar Tarwatsewa – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya sake sukar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari inda ya ce ƙasar ta kama hanyar lalacewa kuma kawunnan ‘yan kasar sun rabu sosai ana zaman ‘yan marina.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a wurin wani taron da kungiyoyi masu wakiltan yankunan kasar suka hallarta.Taron da aka yi a ranar Alhamis 10 ga watan Satumba a Abuja ya samu hallarci kungiyoyi kamar Afenifere, Middle Belt Forum, Northern Elders Forum, Ohanaeze Ndigbo da sauran su.

Tsohon shugaban kasar ya ce bai taba ganin rabuwar kai a Najeriya ba kamar wadda aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Buhari. Ya kuma nuna bakin cikinsa a kan yadda Najeriya ta zama babban birnin talauci na duniya.

“Na ji dadin yadda kuma kuke bakin cikin halin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a yanzu. A yanzu Najeriya ta kama hanyar rugujewa ga kuma rarrabuwar kai; a fannin tattalin arziki kasar mun kama hanyar zama babban birnin talauci na duniya ga kuma rashin tsaro,” kamar yadda Obasanjo ya fadi a wani sashi na jawabinsa.

A cewar tsohon shugaban ƙasar mutane marasa hankali ne kawai za su yi iƙirarin cewa Najeriya ba ta cikin matsala. Ya kuma soki wasu ‘yan siyasa a ƙasar da tun a yanzu sun fara batun zaben shekarar 2023 a maimakon su mayar da hankali wurin gyaran ƙasa.
“Na yi imanin bai dace a bari Najeriya ta ruguje ba muddin za ayi aiki tare, za a iya cimma hakan ta hanyar tattaunawa a maimakon cacar-baki da rikici.
“Wanda ba shi da hankali ne kadai zai yi iƙirarin komai na tafiya dai-dai a Najeriya,” in ji Obasanjo.

Labarai Makamanta