Kungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah ta nuna rashin amincewar ta da furucin da sakataren ta na kasa ya yi akan gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari inda ya kira shi da dan giya mara tarbiya.
Rahotanni sun nuna yadda Masari ya bayyana yana cewa yawancin ‘yan bindiga Fulani ne, furucin da ya tunzura Alhassan har ya caccaki gwamnan.
Ana su bangaren Shugabannin kungiyar na reshen jihar Karsina sun nisanta kansu daga furucin Saleh Alhassan.
Alhassan ya furta munanan kalaman ga gwamnan ne saboda haushin cewa da ya yi yawancin ‘yan bindiga Fulani ne.
A wata hira da aka yi da Gwamna Masari a Channels TV ya ce: “Akwai mutane iri na da suke irin yare na har da irin addini na a cikin su,” “Don haka anan akwai ‘yan bindiga; ba wasu halittu bane na daban, mutane ne da muka sani kuma sun dade su na rayuwa tare da mu tsawon shekaru 100 ma.”
Shugaban Miyetti Allah na jihar Katsina ya ce sakataren ba ra’ayin kungiyar ya fadi ba Sai dai kamar yadda aka ruwaito, a wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da Hassan Kuraye, shugaban kungiyar na jihar Katsina, Alhassan ya fadi son ran sa ne kuma bai nemi izini ba kafin ayi hirar da shi A cewarsa:
“Munyi magana da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na kasa sun ce Alhassan bai bayyana matsayar kungiyar ba dangane da lamarin” Ya dai bayyana ra’ayinsa ne dangane da furucin Masari, Kuraye ya bayar da hakuri a madadin kungiyar ga Masari inda ya bukaci ya yafe musu kuma ya manta da maganganun da sakataren su ya yi akan sa.
Ya ce shugaban kungiyar zai tattaro sauran masu ruwa da tsakin kungiyar a mako mai zuwa don su yi magana da gwamna akan lamarin.