Miyyeti Allah Sun San ‘Yan Bindigar Dake Ta’addanci A Arewa – Shugaban Matasa

An bayyana cewar Ƙungiyar kare muradun Fulani Makiyaya a Najeriya Miyyeti Allah, ta san bata gari cikin Fulani dake ayyukan ta’addanci a ƙasar, sai dai kawai munafunci da kabilanci ne ke ya hana su faɗin gaskiya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Ƙungiyar cigaban matasan Arewacin Najeriya Alhaji Kamal Nasiru Nasiha a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a garin Kaduna.

Nasiru Nasiha ya cigaba da cewar, kyakkyawar hujja akan maganar shi shine abin takaici da bakin ciki da ya faru watannin baya a Sakandaren kwana ta kimiyya dake yankin ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta Jihar Katsina, inda ‘yan bindiga suka sace daruruwan ɗalibai, sai gashi daga baya Gwamnan jihar Zamfara ya fito ya bayyana cewar Ƙungiyar Miyyeti Allah ce ta sa baki aka sako su wanda Ƙungiyar ba ta musa hakan ba.

Shugaban Matasan na Arewa ya bayyana cewar lokaci ya yi da kowa zai bayar da tashi gudummawar wajen ganin an samu nasara akan matsalar tsaro dake addabar yankin Arewa, duba da ganin yadda abubuwa ke ƙara dagulewa a kusan kullum.

Kamal Nasiha ya kuma yaba da kalaman da mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar ya yi a taron da suka yi da kungiyar Miyyeti Allah, inda ya tabbatar musu da cewa a duk cikin mutum goma da aka kama da laifin ta’addanci a arewa takwas daga ciki Fulani.
“Wannan gaskiya ce Sarkin Musulmi ya faɗa, kuma ya dace ya zama izina ga su kungiyoyin Fulani”.

Dangane da hauhawar rashin jituwa da ke wakana yanzu tsakanin Fulani da kabilu a yankin Kudancin Najeriya ne kuwa, Shugaban Matasan na Arewa, yace ya zama dole gwamnati ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen shawo kan matsalar, sannan ya yi kira ga sauran jama’a ‘yan Arewa da kowa ya shiga taitayinshi domin rikicin yana iya naso ya shafi kowa a Arewa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply